Isa ga babban shafi
Egypt

Kotu ta daure Hosni Mubarak

Wata kotun kasar Masar ta yankewa tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak da Wasu Yayyan sa maza guda 2, hukunci shekaru 3 a gidan kaso, tare da cin su tara na Fam miliyan 125.Mubarak da ‘yayansa Alaa da Gamal, an yanke musu hukuncin ne, akan laifin daya shafi, yin almundahana da kudadden Gwamnati, kana kotu ta umarce su da su maido da wasu kudadde daya kai Fam miliyan 21.

Tsohon Shugaban kasar Masar Hosni Moubarak
Tsohon Shugaban kasar Masar Hosni Moubarak REUTERS/Stringer/Files
Talla

Tun a cikin shekara ta 2011 aka cafke mubarak da ‘yayan nasa, bayan hambarar da Gwamnatinsa. Ko a baya an taba yanke musu irin wannan hukunci

Rahotannin dai na cewa watakil lawyansu, ya kara daukaka kara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.