Isa ga babban shafi
Masar

Kotu ta saki mutane 68 a Masar

Wata Kotu a kasar Masar ta sallami mutane 68 daga gidan yari yawancinsu ‘yan raji kare hakkin bil’adama, da ’yan kungiyar yan uwa musulmi, da aka zarga da hannu a cikin hare haren da aka kai wa jami’an tsaro a kasar kamar yadda majiyoyin tsaro da shari’a suka tabbatar.

Sojan kasar Masar
Sojan kasar Masar Photo MONUSCO/Abel Kavanagh
Talla

Mahukuntan kasar Masar sun dade suna nuna halin ba sani ba sabo a kan mabiyan kungiyar ‘yan uwa musulmi tun bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin Mohamed Morsi a 2013 sakamakon zanga zangar da suka yi na nuna rashin amincewa da juyin mulkin.

Jami’an tsaron kasar sun kashe daruruwan mutane a lokutan da suke gudanar da zanga zangar a yayin da dubbai suka kasance a tsare a gidan yari, har ila yau sun kama da dama daga cikin ‘yan kungiyoyin fararen hula tare da matsin lamba a kan masu hankoron kare hakkin dan adam a kasar.

Kotun ta ci tarar kowanne daga cikin mutanen 68 da ta sallama kudin kasar dubu 50 akan laifin halartar zanga zanga da aka haramta a ranar 25 ga watan Janairun 2013 lokacin zanga zangar da ta hambarar da mulkin mulaka’u na shugaba Husni Mubarak.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.