Babban Jami’in ‘Yan uwa musulmi ya rasu a gidan Yari
Wani babban jami’in kungiyar ‘yan uma Musulmi ta Muslim Brotherhood a kasar Masar, ya rasu a lokacin da ake tsare da shi tsawon shekarar guda a gidan Yari. Ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta tabbatar da mutuwar jami’in mai suna Farid Isma’il mai shekaru 58.
Wallafawa ranar:
Isma’il tsohon dan majalisar dokokin kasar ne, kuma jami’I a jam’iyyar Freedom and Justice ta hambararren shugaban kasa Mohammed Morsi, kuma ya wani asibitin birnin Alkahira ne ya rasu, bayan fama da ciwon hanta.
Cikin watan Yulin shekarar 2013 aka fara kame magoya bayan kungiyar ‘yan uwa musulmi, bayan Sojoji sun hambarar da gwamnatin Muhammad Morsi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu