Isa ga babban shafi
Somalia

Dakarun Somaliya sun karbe yankin dake hannun Al-Shebab

Dakarun gwamnatin kasar Somalia tare da tallafin rundunar kungiyar Tarayyar Afrika, sun karbe wani yanki dake hannun ‘yan kungiyar Al-Shebab, mai alaka da Al-Qaeda a yau jumma’a.

Runduna ta musamman dake yaki da ta'addanci a Somaliya
Runduna ta musamman dake yaki da ta'addanci a Somaliya Photo: Reuters
Talla

Ministan tsaron kasar ta Somalia, General Abdulkadir Sheikh Ali Dini ya ce dakarun na gwamnati sun karbe ikon garin Dinsor, ba tare da wata turjiya ba mai tsanani daga mayakan na Al-Shebab.

Tuni dai Mayakan suka baiwa kafarsu iska bayan an yi nasara a kansun a gumurzu da suka tafka da Dakarun.

Wannan na zuwa ne bayan rundunar kungiyar Tarayyar Afrika sun kwato garin Bardhere a ranar larabar data gabata daga hannun mayakan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.