Isa ga babban shafi
Najeriya

Amnesty ta ce Janar Ahmadu Mohammed ya aikata laifukan yaki

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta caccaki matakin da hukumomin Najeriya suka dauka na dawo da Manjo Janar Ahmadu Mohammed daya daga cikin manyan hafsoshin sojin kasar akan mukaminsa bayan an yi masa ritaya

Amnesty International
Amnesty International
Talla

Tun a watan Yunin da ya gabata ne Amnesty International ta bukaci a binciki Manjon Janar Ahmadu Mohammed tare da wasu manyan sojojin Najeriya guda takwas sakamakon zargin su da aikata laifukan yaki da ya hada da kisan mutane sama da dubu takwas, mutanen da aka tsare bayan zarginsu da alaka da mayakan Boko Haram.

Kungiyar ta kara da cewa, akwai cikakkun shaidu da za a gabatarwa kotun hukunta manyan laifuka ta duniya dake birnin Hague domin ta fara gudanar da shari’a.

A cewar Amnesty international, Manjo Mohammed shi ke shugabantar runduna ta bakwai a lokacin da aka zargi sojoji da kashe sama da mutane 640 da aka tsare bayan Boko Haram ta kai farmaki a barikin Giwa da ke birnin Maiduguri na jihar Borno a ranar 14 ga watan Maris na shekara ta 2014.

Har ila yau kungiyar ta Amnesty mai ofishinta a birnin London ta ce, a shekarar 2014 aka yi wa Manjo Mohammed ritaya daga aikinsa akan wani batu na daban sai kuma gashi ta samu labarin mayar da shi bakin aiki a ranar 17 ga watan Janairun wannan shekarar 2016.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.