Isa ga babban shafi
Rash

Rasha ta tabbatar da ingancin maganin riga-kafin cutar Ebola

Hukumomi a kasar Rasha sun ce gwajin da aka yi na maganin cutar Ebola da ta samar watanni 15 da suka gabata ya nuna inganci, kuma za’a ci gaba da gwada shi a kasashen dake Yammacin Afirka.

Jami'in kiwon lafiya dake aikin kula da masu cutar Ebola a kasar Guinea
Jami'in kiwon lafiya dake aikin kula da masu cutar Ebola a kasar Guinea KENZO TRIBOUILLARD / AFP
Talla

Ministar lafiyar Rasha Veronika Skovortsova tace anyi gwajin maganin sau biyu a Rasha akan wasu mutane da suka bada kan su kuma gwajin ya nuna inganci sa.

Skovortsova tace maganin mai suna GamEvac-Combi a hada shi ne a Cibiyar binciken cututtukar gwamnati kuma za’a kai shi kasar Guinea dan ci gaba da gwaji.

Kasashen Guinea, Liberia da Saliyo sun fuskanci matsananciyar cutar wadda ta lakume rayukan mutane sama da 11,300.

Ministar dai na wannan bayani ne kafin taron da za tayi da shugabar Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, Margareth Chan a gobe talata a birnin Geneva.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.