Isa ga babban shafi
Rwanda

Kagame ya kare matakinsa na tazarce

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ya kare kansa dangane da zaben jin ra’ayin jama’a da zai ba shi damar tsawaita zamansa akan karagar mulki har zuwa shekara ta 2034, matakin da ya gamu da suka daga Amurka da sauran kasashen Yamma masu karfin fada a ji.

Shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame.
Shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame. DR
Talla

Shugaba Kagame, wanda ke rike da madafun ikon kasar tun shekara ta 1996 ya ce, ya na aiki ne da ra’ayin al’ummar kasar da suka kada kuri’ar a watan Disamban bara.

A watan da ya gabata ne Amurka ta bayyana damuwarta akan shirinsa na yin tazarce domin neman wa’adi na uku.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.