Kotu ta yi watsi da karar da Pistorius ya shigar
Kotu a kasar Afirka ta Kudu ta yi watsi da karar da Oscar Pistorius tsohon zakaran gudun nakasassu na dunya ya shigar, inda yake neman a sassauta hukuncin dauri da aka yanke masa bayan ya amince da cewa shi ne ya kashe masoyiyarsa Reeva Steenkamp.
Wallafawa ranar:
Wannan dai ita ce damar karshe da Pistorius ke da ita domin ganin cewa an soke hukuncin daurin da aka yanke masa.
Yanzu dai dan wasan zai fuskanci hukuncin akalla daurin shekaru 15 a gidan yari sakamakon kisan budurwar tasa a ranar 14 ga watan Fabairun shekarar 2013, wato a ranar masoya, ta hanyar harbin ta da bindiga amma ya ce, lamarin ya faru ne cikin kuskure.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu