Isa ga babban shafi
Sahel

Ministocin Sahel na taro kan tsaro a N'djamena

A yau juma’a ministocin tsaro na kasashen yankin Sahel 5 da suka hada da Mauritania da Mali da Burkina Faso da Nijar da kuma Chadi, na gudanar da taro a birnin N'djamena na Chadi, domin bitar irin ci gaban da ake samu ta fannin tsaro a cikin kasashensu.

Ministocin kasashen yankin Sahel na taro kan tsaro a birnin N'djamena na kasar Chadi
Ministocin kasashen yankin Sahel na taro kan tsaro a birnin N'djamena na kasar Chadi Agrhymet/FAO
Talla

Kafin wannan zama da ministocin za su yi a yau, manyan hafsoshin sojin kasashen ne suka gudanar da taron share fage, domin duba irin ci gaban da ake samu ta fannin fada da ayyukan ta’addanci a yankin na Sahel.

Kasashen dai na fama da hare haren ta'addanci musamman daga kungiyoyin da ke da'awar jihadi, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a tsawon shekaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.