Isa ga babban shafi
Syria-MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta rasa ma'aikata 50 a Syria

Ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya sama da 50 sun mutu yayin da wasu daga ciki suka bata a lokacin da suke gudanar da ayyukansu a kasar Syria mai fama da yakin basasa

Jami'in agajin Red Cross a Syria
Jami'in agajin Red Cross a Syria REUTERS/Stoyan Nenov
Talla

A sanarwar da ta biyo bayan ranar bikin nuna hadin kan ma’aikatan Majalisar ne aka bayyana yawan mutanen da suka rasa rayukansu a yayin rikicin kasar Syria na sama da shekaru 4

Ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya sama da 50 din ko sun bata ne kokuma wadanda suka rasa rayukansu ko kuma wadanda ke tsare a gidajen yarin kasar ba bisa ka’ida ba

Akwai ma ma’aikatan kungiyar Red Cross da wasu ma’aikatan kungiyoyi masu zaman kansu da suka rasa rayukansu kokuma aka dadde ba’a san inda suke ba.

Rahotan nay au juma’a ya ci gaba da cewa akwai daruruwan jami’an kiwon lafiya da suka rasa rayukansu a yayin gudanar da ayyukansu, Kevin Kennedy wani jami’In hukumar samar da agaji a Syria ya bayyana al’amarin a matsayin abin tsoro inda ya yi kira ga bangarorin dake rikici da juna a Syria da su samar da hanyar kare ma’aikata dake aiki jin kai tare da sakin jami’an Majalisar Dinkin Duniya dake tsare a gidajen yarin kasar

A daya bangaren kuma mutane sama da 300,000 ne yakin Syriya ya lakume baya ga dubban al’ummar da suka tserewa rikicin kasar zuwa nahiyar Turai da yanzu haka ya haifar da matsalar ‘yan gudun hijra mafi muni a tarihi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.