Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Za a fara muhawarar tsige Jacob Zuma

Majalisar dokokin Afrika ta Kudu za ta fara mahawara kan bukatar tsige shugaban kasar Jacob Zuma a  gobe Talata. 

Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma
Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma DAVID HARRISON / AFP
Talla

Wannan dai na zuwa ne bayan babbar kotun kasar ta same shi da laifin taka kundin tsarin mulki wajen amfani da kudin talakawa domin fadada gidansa.

Shugaban majalisar Baleka Mbete ne ya sanar da zaman muhawarar sakamakon hukuncin na kotun da ta umurci Zuma ya mayar da wani kaso na Dala miliyan 16 da ya yi amfani da su cikin kwanaki 45 masu zuwa.

Mmusi Maimane, shugaban Jam’iyyar adawa ta Democratic Alliance ya gabatar da kudirin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.