Mutane 100,000 sun fice Darfur
Majalisar Dinkin Duniya tace akalla mutane sama 100,000 suka gudu suka bar gidajensu a yankin Darfur na Sudan sakamakon wani sabon tashin hankalin da aka samu tun daga watan Janairun da ya wuce.
Wallafawa ranar:
Shugaban aikin samar da zaman lafiya Herve Ladsous ya sanar da haka a jawabin da ya ke yi wa kwamitin Sulhu, yana mai cewar matsalar ta fi kamari ne a Jabel Marra, inda ake ta samun hare haren sama.
Ladsous ya ce akalla mutane 138,000 suka fice yankin Jabel Marra da ke karkashin ikon ‘Yan tawayen SLA da Abdulwahid Nur ke jagoranta
Sai dai Jakadan kasar Sudan a Majalisar Omar Dahab Fadi ya musanta rahotan inda yace mutanen yankin da dama da fadan a baya ya sa suka bar gidajensu sun dawo, kuma yanzu haka suna noma.
Sama da mutane 300,000 Majalisar Dinkin Duniya ta kisyasta an kashe a rikicin Darfur tun a 2003.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu