Isa ga babban shafi
Darfur-Sudan

zaben raba gardama a Darfur

Al’ummar yankin Darfur na kasar Sudan na gudanar da zaben raba gardama domin tabbatar da matsayin su duk da cewa wasu kasashen duniya na sukan lamari.

Omar el-Beshir Shugaban kasar Sudan a yankin Darfur
Omar el-Beshir Shugaban kasar Sudan a yankin Darfur Reuters
Talla

Zaben raba gardaman wanda aka fara a jiya littini, kuma za’ ayi kwanaki uku ana gudanarwa, ya kasance ‘yan tawaye na kaurace masa, kuma akwai wasu dake sansanonin ‘yan gudun hijira dake adawa da zaben.

Shugaban Sudan Omar al-Bashir, wanda kotun kasa-da-kasa ke nema ruwa ajallo, ya nace da sai anyi wannan zabe, don neman ra’ayoyin jama’a ko akwai bukatar hada jihohi 5 dake yankin Darfur, ko kuma su tsaya amatsayin da suke.

Hadewar yankin Darfur don ta kasance yanki na daga cikin bukatun ‘yan kabilu kanana dake yankin , inda suke ta yakar Gwamnatin Sudan, tun shekara ta 2003, amma kuma sun kauracewa zaben, saboda zargin ba ayi daidai ba.

Amurka ta nuna damuwa, inda take gargadin cewa muddin akayi karkashin dokokin yanzu babu yadda za ayi adalci.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.