Kotu A Kasar Africa ta Kudu Za Ta Sake Duba Zargin Almundahana 800 Da Ake Yiwa Shugaba Jacob Zuma
Wata Kotu a kasar Africa ta Kudu ta ce Shugaban kasar Jacob Zuma zai fuskanci zargin laifukan cin hanci da rashawa 800 wadanda aka jingine tun shekara ta 2009.
Wallafawa ranar:
Zargin wanda ya shafi miliyoyin kudade wajen sayen makamai, Mai shigar da kara ya jingine su ne domin baiwa shugaba Jacob Zuma damar tsayawa takarar shugabancin kasar a wancan lokaci.
Alkalin kotu dake Pretoria, Aubrey Ledwaba ya bayyana cewa sun jingine karar a wancan lokaci amma yanzu ya dace a sake duba batun.
A cewar mai shigar da kara tilas aka jingine karar saboda katsalandan cikin shari'ar da wasu ‘yan siyasa ke yi, kamar yadda aka saurare su a zantuka ta wayoyin sadarwan su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu