An soma zaman shawo kan rikicin Burundi
A yau asabbbar an bude taron tattauna samar da sulhu a Burundi, kasar da kwanciyar hankali ya gaggara samuwa tsawon shekara guda, tun lokacin da Shugaba Pierre Nkurunziza ya tsaya takarar shugabanci.
Wallafawa ranar:
Zaman tattaunawa da ake gudanawar a Tanzania, ya samu halarta jami’an gwamantin Burundi, dana Diflomasiya da kuma wakilan kungiyoyin fararan hula.
Sai dai ba a gayyace babban kungiyar adawar kasar ba, a tattaunar da za a kai 24 ga watan Mayu ana gudanar da ita.
Rikicin siyasar Burundi ya lakume rayukan al'ummar kasar da dama tare da tilastawa wasu hijira zuwa kasashen dake makwabtaka da su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu