Isa ga babban shafi
Nijar

An tsinci gawarwakin ‘Yan ci-rani 34 a Nijar

Gwamnan Jamhuriyar Nijar ta sanar da gano gawawakin wasu bakin haure 34 da ke neman ratsa kasar zuwa Turai a Yankin Sahara. Sanarwar da gwamnatin ta fitar tace an gano mutanen ne a Assamaka kan iyaka tsakanin Nijar da Algeria.

Dubban mutanen Afrika ne ke ratsawa ta Agadez a Nijar domin tsallakawa zuwa Turai
Dubban mutanen Afrika ne ke ratsawa ta Agadez a Nijar domin tsallakawa zuwa Turai REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

Ma’aikatar cikin gidan Nijar tace mutanen sun mutu ne saboda matsanancin kishir-ruwa.

Ministan cikin gida Bazoum Muhammed ne ya sanar da gano gawarwakin bayan wanda ke safarar su ya gudu ya bar su tsakanin 6 zuwa 12 ga watan Yuni.

Sanarwar tace 20 daga cikin ‘Yan ci ranin yara ne kanana, kuma daga cikinsu kawai manyan mata 9 da Maza 5 da ke kokarin ratsa sahara zuwa Turai.

Sanarwar ta kara da cewar an gano biyu daga cikin mamatan a matsayin ‘Yan Najeriya ne, yayin da ake kokarin gano inda sauran suka fito.

Kungiyar da ke sa ido kan masu yin Kaura ta IOM tace a bara kawai baki kusan 120,000 suka ratsa Nijar ta Agadez zuwa Turai, kuma 37 daga cikinsu sun mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.