Sojojin Liberia sun karbi ragamar tafiyar da tsaro
Sojojin kasar Liberia sun karbi ragamar samar da tsaro a kasar a karon farko tun bayan kawo karshen yakin basasa, shekaru 13 da suka gabata. Majalisar Dinkin Duniya na shirin janye dakarunta 4,000 da suka rage a kasar daga cikin 15,000 da aka girke na tsawon lokaci.
Wallafawa ranar:
Za a bar kadan daga cikin dakarun Majalisar Dinkin Duniya wadanda zasu dinga taimakawa idan halin hakan ya yi.
A baya an rusa rundunar ‘Yan Sanda da sojin kasar saboda rawar da suka taka na goyan bayan bangarorin yakin basasar kasar, matsalar da ta jefa kasar cikin tashin hankali mai tsanani.
Sojojin gwamnati da ‘Yan tawaye sun yi wa mata fyade tare da kisan daruruwan mutane a rikicin kasar tsakanin 1989 zuwa 2003.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu