Isa ga babban shafi
LIBERIA

WHO ta ce an kawo karshen Ebola a Liberiya

A gobe alkhamis Hukumar lafiya ta Duniya za ta sanar a hukumance wanke kasar Liberiya daga cikin kasashen Yammancin Africa da suka yi nasarar yakar cutar Ebola mai saurin hallaka mutum

Gawar wanda Ebola ta hallaka
Gawar wanda Ebola ta hallaka Reuters/路透社
Talla

Nan bada daddewa ba hukumar lafiya ta Duniya za ta sanar a hukumance nasarar kasar Liberiya na yakar cutar Ebola, hakan na nufin babu cutar baki daya a kasar

Mutane sama da dubu hudu cutar Ebola ta hallaka a kasar ta Liberiya kafin a kai ga samun wannan nasarar acewar hukumar lafiya.

Cutar Ebola da ta bulla a wasu kasashen yammancin Afrika da suka hada da Saliyo da Guinea da Liberiya ta hallaka mutane sama da dubu goma sha daya a tsawon shekaru biyu da aka yi ana ta yaki da cutar

Sai dai wani gudun ba hanzari ba, ana fargabar cewar akwai yiyuwar sake samun bullar cutar a kasar ganin cewa wannan bashi bane karon farko da ake tabbatar da kawo karshen annobar,inda a wasu lokuta ake sake samun sabbin mutane da suka kamu da cutar

Amman  ganin yadda aka hada karfi da karfe wajen yakar cutar akwai tabbacin cewa Liberiya ta yi bankwana da wannna cutar dake haddasa tsiyayar jini a jikin dan adam, al’amarin dake kai ga rasa rai cikin kankanin lokaci
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.