Ana zaben kananan hukumomi a Afrika ta kudu
Alummar kasar Africa ta Kudu na gudanar da zabukan kananan Hukumomi a yau Laraba, a wani mataki da zai gwada karfin Jam’iyyar da ke mulki ta ANC.
Wallafawa ranar:
Ana ganin zaben tamkar zakaran gwaji daji ga gwamnatin Jacob Zuma da ke fuskantar suka a Afrika ta kudu kan zargin rashawa da tabarbarewar tattalin arziki.
Jam’iyyar ANC dai na iya shan kaye a zaben ko kuma rasa samun kuri’u a wasu mazabun, da watakila suka hada da manyan biranen kasar kamar Pretoria, da Johannesburg da birnin Port Elizabeth.
Ganin yadda tattalin arzikin kasar ke cikin wani hali da kuma rashin ayyukan yi ga matasaa, Jami’yyun adawa na ganin za su bada mamaki a zaben.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu