Isa ga babban shafi
Libya

Sojojin Libya sun sake kaddamar da hari kan Sirte

Sojojin da ke biyayya ga gwamnatin Libya mai samun goyon bayan majalisar dinkin Duniya, sun kaddamar da sabbin hare-hare, kan mayakan ISIL da suka ja tunga a garin Sirte don karbe garin.

Sojin Libya suna kara kusantar garin Sirte
Sojin Libya suna kara kusantar garin Sirte Reuters/路透社
Talla

Garin na Sirte dai na a matsayin tunga ta karshe kuma mafi karfi da Mayakan ISIL din suka kafa, wanda kuma rasa ta zai zama Karin koma baya garesu, wadda tuni ISIL din ke shan kashi a kasashen Iraqi da Syria.

Kawo yanzu sojin Libya da taimakon luguden wutar jiragen yakin Amurka, sun samu nasarar kwace kusan dukkanin yankunan da suke karkashin mayakan na ISIL.

Wani mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Amurka Kaftin Jeff Davis ya ce dudu mayakan da suka rage cikin garin na Sirte basu kai dari uku ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.