Isa ga babban shafi
Libya

Majalisar Libya ta ki amincewa da gwamnatin hadin-kai

Majalisar dokokin Libya ta yi watsi da halaccin gwamnatin hadin-kan kasar da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, a wani mataki da ake ganin zai dagula kokarin da ake na kawo karshen rikicin kasar.

Dakarun gwamnatin Libya da ke fada da IS
Dakarun gwamnatin Libya da ke fada da IS REUTERS/Stringer
Talla

Mai magana da yawun majalisar wadda ita ma majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita, Adam Boussakhra ya ce a zaman da suka yi a yau Litinin, ‘yan majalisar sun ce ba su amince da shugabancin gwamnatin da ke karkashin Fayez Al-Sarraj ba.

Wannan na zuwa ne a yayin da Dakarun gwamnatin Libya suka sanar da yin nasarar kwace wasu muhimman unguwanni daga hannun mayakan Daesh a garin Syrte, inda suka kwace wani gidan yari da kungiyar ke tsare da jama’a a cikinsa.

Mafi yawan dakarun da suka fatattaki mayakan na Daesh sun fito ne daga Misrata, kuma kakakinsu Akram Gilwan ya ce za su ci gaba da kokarin ganin cewa sun kwato illahirin birnin daga hannun ‘yan ta’adda.

Amincewa da gwamnatin hadin-kai dai mataki ne da ake ganin zai magance rikicin Libya da ke fama da mayakan IS masu da’awar jihadi.

Amma ‘Yan Majalisar sun kada kuri’ar kin amincewa da gwamnatin hadin-kan.

‘Yan majalisa 61 ne suka kada kuri’ar kin amincewa da halaccin gwamnatin yayin da 36 suka kauracewa zaman majalisar.

An dade dai ana jiran majalisar ta kada kuri’ar domin tabbatar da hadin kan bangaren gwamnatin da ke iko a gabashin Libya.

Wannan matakin dai zai dada jefa Libya cikin wani sabon rikici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.