Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta tabbatar da mutuwar sojinta a Libya

Shugaban Faransa Francois Hollande ya tabbatar da mutuwar sojojin kasar guda uku wadanda ke aikin tattara bayan sirri a kasar Libya.

Shugaban Faransa Francois Hollande da wata tawagar jami'an tsaro
Shugaban Faransa Francois Hollande da wata tawagar jami'an tsaro REUTERS/Stephane de Sakutin
Talla

Hollande ya ce, sojojin sun gamu da hadari ne lokacin da suke aikin tattara bayanan sirri mai sarkakiya a kasar Libya sakamakon faduwar jirginsu.

Kasar Faransa na daga cikin kasashen da suka jagoranci kungiyar NATO wajen taimaka wa 'yan tawayen Libya kifar da gwamnatin shugaba Muammar Ghadafi a shekarar 2011.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.