Isa ga babban shafi
Gabon

Ranar ta karshe ga masu kalubalantar zaben Gabon

Yau ce rana ta karshe da aka ware dan shigar da kara domin kalubalanatar zaben shugaban kasar Gabon da aka yi wanda ya haifar da tashin hankali.

Shugaban 'yan adawar Gabon Jean Ping
Shugaban 'yan adawar Gabon Jean Ping AFP/Marco Longari
Talla

Ya zuwa yanzu dai shugaban ‘yan adawar kasar Jean Ping bai sanar da ko zai shigar da kara ba saboda abin da ya kira rashin amincewa da kotun.

Ping ya bukaci magoya bayansa su gudanar da zanga zangar lumana dan nuna rashin amincewar su da sakamakon zaben.

Kungiyar kasahsen Afrika ta AU ta ce a shirye ta ke ta sasanta bangarorin da ke rikici a kasar.

A ranar talata Faransa ta bukaci a sake kidaya kuri'un zaben domin lafar da kurar rikicin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.