Isa ga babban shafi
Gabon

Yau ake rantsar da Ali Bongo na Gabon

A wani lokaci a yau za a rantsar da Ali Bongo a matsayin shugaban kasar Gabon bayan da kotun tsarin mulkin kasar ta tabbatar da nasararsa a kan abokin adawarsa Jean Ping.

Kotun fasalta kundin tsarin mulkin Gabon
Kotun fasalta kundin tsarin mulkin Gabon RFI/Richard Riffonneau
Talla

Ali Bongo mai shekaru 53, ya samu sama da kashi 50%, yayin da abokin hamayyarsa Jean Ping ya samu kashi 47%.

A satin da ya gabata, lokacin da ake dakon hukuncin da kotun fasalta kundin tsarin mulkin kasar za ta yanke kan zaben shugaban kasar, ‘yan adawa magoya bayan Jean Ping, sun zargi kotun da yunkurin yi musu rashin adalci.

Tun da fari bayan sanar da nasarar shugaba Ali Bongo, Jean Ping ya bijirewa sakamakon, sai dai a wani mataki na gwamnatin kasar, ta ce zata dora alhakin duk wani tashin hankali da ya auku kan Ping da mogaya bayansa, bayan baza ‘yan sandan kwantar da tarzoma da ta yi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.