Isa ga babban shafi
Habasha

An kafa dokar ta-baci a Habasha

Gwamnatin Habasha ta kafa dokar ta baci bayan shafe kwanaki ana zanga-zangar dawa da gwamnati. Majalisar Ministocin kasar ce ta amince da kafa dokar sakamakon hasarar rayuka da dukiya da aka samu a kasar.

'Yan Kabilar Oromo da ke zanga-zangar kyamar gwamnati a Habasha
'Yan Kabilar Oromo da ke zanga-zangar kyamar gwamnati a Habasha Reuters/Tiksa Negeri
Talla

Mutane da dama ne dai suka mutu a arangamar da aka yi tsakanin ‘yan sanda da masu zanga-zagngar a makon jiya.

Habasha dai ta shafe shekaru tana fama da zanga-zangar kyamar gwamnati daga ‘yan kabilar Oromo da Amhara da suke ganin an mayar da su saniyar ware a gwamnatin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.