Isa ga babban shafi
Habasha

Habasha na zargin wasu kasashe kan rikicinta

Gwamnatin Habasha ta bayyana cewa, makiya daga kasashen ketare ne suka haddasa zanga-zangar da ta tilasta mata kafa dokar ta baci har tsawon watanni shida.

Masu zanga zanga a birnin Addis Ababa na kasar Habasha
Masu zanga zanga a birnin Addis Ababa na kasar Habasha REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Mai magana da yawun gwamnatin Habasha, Getachew Reda ya bayyana cewa, suna zargin kasashe kamar Masar da Eritrea da bai wa masu zanga zangar tallafin kudi da horo da kuma makamai.

Gwamnatin kasar dai na fuskantar kalubale mafi girma a cikin shekaru 25 da suka wuce, in da al’ummar kasar ke nuna mata adawa saboda zargin ta da gudanar da mulkin kama-karya ta hanyar kwace filayensu da sunan habbaka masa’aantu a kasar.

A jiya Lahadi ne, aka kafa dokar ta baci bayan tashe-tashen hankulan fiye da shekara guda a yankunan Oromiya da Amhara da ke kusa da babban birnin Addis Ababba.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun bayyana cewa, kimanin mutane 500 ne suka mutu sakamakon wasu rikice-rikice da suka hada da arangama tsakanin jami’an ‘yan sanda da masu zanga-zagngar.

Har ila yau, zanga-zangar ta yi sanadiyar lalacewar masana’antu da dama mallakin kasashen ketare, bayan masu gangamin sun soki kamfanonin saboda siyan filayen da gwamnnatin ta kwace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.