Britaniya za ta soma karbar yara 'yan gudun hijra
Bayan cimma jituwa Britaniya ta amince ta soma karbar wasu daga cikin yaran dake a sansanin ‘yan gudun hijra a Faransa inda za ta meka su ga danginsu da suka yi nasarar ketarawa kasar
Wallafawa ranar:
Ana kuma shirin yin hakan nan ne nan ba da jimawa ba bayan cimma jituwa a tsakanin kasashen biyu.
Dubban ‘yan gudun hijra ne dai ke jibge a sansanin Calais dake kasar Faransa da a kullum suke yunkurin shiga Brittaniya dama wasu kasashen nahiyar Turai, akwai kuma yara da dama acikinsu.
Yanzu an soma yiwa yaran da ake ganin danginsu na Britaniya rijista kafin hada su da iyayensu akwai kuma wasu da ake kokarin tantancewa don ganin ko sun cancanci basu mafaka a kasar.
Wannan na zuwa ne a yayin da Faransa ke shirin kulle sansanin na Calais sai dai a daya bangaren Hukumar ‘yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana fargaba cewar akwai yiyuwar yin fataucin yara.
Daruruwan yara da yaki ya raba da iyayensu ne ke rayuwa a sansanin ba tare da sanin inda iyayensu suke ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu