An cafke mutane da dama a zanga-zangar kyamar baki a Calais
‘Yan sanda a Faransa sun sanar da cafke mutane 14 a lokacin zanga-zangar nuna kyamar baki da aka yi a wannan asabara garin Calais, wanda ba ya da nisa da iyakar kasar da Birtaniya.
Wallafawa ranar:
Rahotanni sun ce kusan mutane 80 ne suka shirya wannan zanga-zanga ba tare da sun samu izinin hukuma ba, inda suka kange wasu gadoji biyu da ke birnin, inda suke nuna rashin amincewarsu da tsugunar da ‘yan ci rani a yankin.
Mai magana da yawun gwamantin lardin na Calais Etienne Desplanques, ya ce wasu daga cikin masu tarzomar sun kona tayoyi a kan tituna, tare da hanawa jama’a gudanar da zirga-zarga kafin jami’an tsaro su tarwatsa su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu