Isa ga babban shafi
Rwanda

Kasashe 150 sun cimma matsaya kan tunkarar matsalar dumamar yanayi

Wakilan kasashe sama da 150 ne suka hallara a kasar Rwanda inda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar da ta shafi yadda za a tunkari matsalar dumamar yanayi a duniya

Kasashe fiye da 150 ne suka amince da tunkarar matsalar da dumamar yanayi ke haifarwa a duniya
Kasashe fiye da 150 ne suka amince da tunkarar matsalar da dumamar yanayi ke haifarwa a duniya Clément GUILLAUME/Getty Images
Talla

Wannan zai bayar da damar yi wa yarjejeniyar birnin Montreal da aka kulla a baya kwaskwarima ganin dukkanin kasashen musanman masu hannu da shuni sun amince su rage yawan turirin da ke gurbata yanayi a duniya.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da ya taimaka wajen cimma yarjejeniyar ya ce wannan abin alfahari ne ga dukkan Duniya.

Bincike dai ya nuna cewa yawan hayakin da ake fitarwa a sanadiyar ababen hawa da girki da wasu hanyoyi na anfani da wasu na'urar abinci na taka mahinmiyar rawa a gurbata yanayi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.