Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya

Ana zanga-zangar adawa da dakarun MDD a Bangui

An yi arangama tsakanin dakarun Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya da wasu daruruwan mutane da ke gudanar da zanga-zangar neman a janye dakarun daga kasar.

Dakarun MINUSCA da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Afrika ta tsakiya
Dakarun MINUSCA da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Afrika ta tsakiya ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Da farko dai daruruwan mutane ne suka taru a wani dandali da ke tsakiyar birnin Bangui, inda nan take wasu suka fara jifar dakarun na Majalisar Dinkin Duniya da duwatsu, kafin daga bisani wasu ‘yan bindigar suka fara buda wuta a kan dakarun.

Shaguna da Bankuna sun kasance a rufe a Bangui bayan masu zanga-zangar sun toshe hanyoyi tare da kone konen tayu.

Wasu kungiyoyin fararen hula ne suka kira zanga-zangar ta rana guda a Bangui domin neman ficewar MINUSCA 12,000 a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya, da suka ce sun gaza gudanar da aikin da ya rataya akan su na wanzar da zaman lafiya.

Dakarun MINUSCA dai sun yi harbi sama domin razana masu zanga-zangar a lokacin da suka nufi shalkwatarsu a Bangui.

Tun a 2013 Afrika ta tsakiya ke fama da rikici mai nasaba da addini da kabilanci bayan mayakan Seleka musulmi sun hambarar da gwamnatin Francois Bozize Kirista, matakin da ya haifar da mayakan anti-balaka yakar Seleka.

Dubban mutane suka mutu a rikicin kafin Majalisar Dinkin Duniya ta aiko da dakarun wanzar da zaman lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.