Isa ga babban shafi
Kenya

An gargadi Kenya kan yunkurin rufe sansanin Dadaab

Sashin kula da ‘yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya, ya gargadi gwamnatin Kenya, game da yunkurin da take yi na rufe 'Dadaab', sansanin ‘yan gudun hijira mafi girma a duniya.

Wani jariri da yunwa ta kassara a sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab da ke Kenya
Wani jariri da yunwa ta kassara a sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab da ke Kenya
Talla

Wani rahoto da sashin Majalisar ya fitar ya nuna cewa, shirye shiryen rufe sansanin da hukumomin Kenya ke yi zai tilastawa masu gudun hijira daga Somalia komawa kasarsu wadda a yanzu haka ke fama da tashin hankali, sakamakon zafafar hare haren mayakan al Shabaab.

Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar da jami’an Majalisar Dinkin Duniya suka zanta da su, sun ce mai yiwuwa ne su gwammace komawa Somalia duk da matsananciyar yunwa da zasu fuskanta a kasar.

Hukumar kula da masu gudun hijirar karkashin Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Kenya ta dage aniyar rufe sansanin a ranar 30 ga watan Nuwamba, kamar yadda ta tsara.

Sansanin Dadaab da ya shafe shekaru 25 da kafuwa, yana dauke da ‘yan gudun hijira sama da 250,000.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.