Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu-Kenya

Kenya ta fara janye dakarunta daga Sudan ta Kudu

Kasar Kenya ta fara janye dakarunta daga Sudan ta Kudu, bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta zargi babban kwamandan dakarun kasar da nuna sakaci wajen bayar da kariya ga fararen hula a kasar ta Sudan.

Tawagar farko ta sojojin kasar Kenya sun soma janyewa daga kasar Sudan ta Kudu
Tawagar farko ta sojojin kasar Kenya sun soma janyewa daga kasar Sudan ta Kudu REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

Kashi na farko na sojojin kasar ta Kenya da suka koma gida a wannan laraba ya kai dakaru dari daya daga cikin dakaru sama da dubu daya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu.

Kenya dai ta dauki wannan mataki ne domin nuna rashin jin dadinta dangane da matakin da MDD ta dauka na korar babban kwamandan dakarun kasar Johnson Mogoa Kimani Ondieki, wanda aka zarga da laifin kin bayar da kariya ga fararen hula.

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya ce bai ji dadin matakin na MDD ba, inda ya ce bai kamata a dora wa dakarun kasar alhakin gazawar da sauran dakaru na kasashen duniya suka yi ba.

Janye dakarun dai ba karamin gibi zai bari ta fannin tsaro a Sudan ta Kudu ba, kasar da ke fama da yakin basasar da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da tilasta wa wasu dubbai barin gidajensu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.