Isa ga babban shafi
Gambia

Jammeh ya soke yin zanga-zanga bayan zaben Gambia

Shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh ya ce babu wata zanga-zanga da za a amince da ita bayan zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar Alhamis. A yayin da dan takarar adawa ke samun goyon baya a gangamin yakin neman zaben shi a Banjul.

Zanga-zangar 'Yan adawa a Gambia
Zanga-zangar 'Yan adawa a Gambia AFP/Stringer
Talla

Jammeh ya ce dan adawar ba zai ci zabe ba inda ya ce babu dalilin yin zanga-zanga domin ba za a yi magudi ba.

Gangamin yakin neman zaben dan takarar Jam’iyyar adawa Adama Barrow ya nuna barazana ne ga shugaba Yahya Jammeh wanda ke mulkin kasar tun a 1994 da ya kwace mulki da karfi.

Masu sharhi dai na ganin Jammeh na fuskantar babbar barazanar da bai taba gani ba tun hawan shi mulki.

Dan Takaran Adama Barrow da ke adawa da Jammeh ya bayyana fatar samun nasara musamman ganin irin kaunar da ya samu daga al’ummar Gambia.

Bayan kammala yakin neman zaben sh, Barrow ya ce irin magoya bayan da ya gani, yana da yakinin cewar zai kada shugaba Yahya Jammeh a zaben.

Sau hudu ne dai Shugaba Jammeh ke lashe zaben Gambia bayan juyin mulkin shekarar 1994 da kwaci mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.