Isa ga babban shafi
Gambia-Amnesty

‘Yan adawa na zaman Zullumi a Gambia inji Amnesty

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta bayyana cewa Kasar Gambia ta shiga cikin jerin kasashen duniya, inda ‘yan adawa ke zaman zullumi ganin yadda ake samun yawaitan kame da azabtar da duk wani wanda ya nemi sukan Gwamnatin Shugaba Yahya Jammeh.

Shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh
Shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh AFP PHOTO / SEYLLOU
Talla

A cewar Amnesty ‘yan siyasa, manema labarai, kungiyoyin kare ‘yancin bil’adama, da wasu shugabannin addinai, basu tsira ba daga tursasawa, gabanin babban zaben kasar, inda shugaba Yahya Jammeh ke hankoron zarcewa da iko karo na biyar.

Amnesty ta ce jami’an tsaro na musamman ake amfani dasu domin hana duk wani mutum fadin ra’ayinsa a fadin kasar.

Kungiyar Amnesty ta ce mutane, da ake kamawa a kan nemi su bayar da lambobin bude shafukansu na wasiku da dukkan kafofin su na sada zumunci, duk dai domin hana adawa.

A shekarar 1994, Shugaba Yahya Jammeh ya kwace iko a juyin mulkin da babu zubda jinni, kuma har yanzu zarensa yake ja.

A dan tsakanin ma har cewa yake yi Babban Sakatare Janar na MDD Ban Ki-moon dama kungiyar Amnesty, su je duk inda zasu, saboda kawai sun nemi a yi binciken kisan masu bore a cikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.