Isa ga babban shafi
Gambia

Jammeh ya sha kaye a zaben Gambia

Dan takarar adawa a kasar Gambia Adama Barrow ya yi nasarar lashe zaben shugabancin kasar da aka gudanar a jiya alhamis, inda ya samu sama da kashi 45 cikin dari na kuri’un da ake jefa.

Shugaba Yaya Jammeh ya amsa shan kaye a zaben Gambia
Shugaba Yaya Jammeh ya amsa shan kaye a zaben Gambia ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Tuni dai shugaban kasar mai-ci Yahya Jammeh da ya samu kuri'u 36 cikin 100, ya amince da shan kaye a wannan zabe, bayan share tsawon shekaru 22 a kan karangar mulkin kasar.

Shugaban hukumar zaben kasar ya ce amincewa da shan kaye da Yahya gammeh ya yi wani abu ne da ba a saba ganin ba kuma ya zo musu da mamaki.

A wani lokaci nan gaba ake saran Shugaba Jammeh ya gabatar da Jawabi ta kafar talabijin kasar domin ta ya abokin takarasa murnar nasara.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.