Isa ga babban shafi
Ghana

Al'ummar Ghana na dakon sakamakon zabe

Al’ummar Gahana na ci gaba da dakon sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a jiya Laraba, in da hankula suka fi karkata kan shugaba mai ci John Dramani Mahama da kuma babban abokin hamayyarsa Nana Akufo-Addo.

Al'ummar Ghana na dakon sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu
Al'ummar Ghana na dakon sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu REUTERS/Luc Gnago
Talla

Kawo yanzu dai babu wani hasashen da ke nuna wanda zai iya lashe zaben tsakanin Mahama da Akufo-Addo.

A yammacin yau ne za a sanar da wadanda suka yi nasara a zaben na shugaban kasa da kuma na ‘yan majalisu.

Da misalin karfe 5 na yammacin jiya aka rufe rumfunan zabe, yayin da hukumar zaben kasar ta dage kada kuri’u a yankin Jaman North zuwa yau Alhamis saboda matsalar tsaro.

Masu sa ido sun bayyana cewa an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali duk da cewa fafatawa ta yi zafi tsakanin Mahama da Akuffo-Addo.

Shugaba Mahama na neman wa'adi na biyu ne, yayin da Akuffo-Addo ke caccakar sa saboda matsalar tattalin arziki da kasar ta fada a ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.