Isa ga babban shafi
Gambia

Al'ummar Gambia sun soma komawa Gida

Al’ummar Gambia da suka tsere daga kasar saboda kaucewa tashin hankali sakamakon rikicin zaben kasar sun fara komawa gida.

Al'ummar Gambia na komawa Gidajensu
Al'ummar Gambia na komawa Gidajensu REUTERS/Emma Farge
Talla

A karshan makon da ya gabata bayan amincewar Yahya Jammeh na ficewa daga kasar, sabon shugaba Adama Barrow ya yi kira ga ‘yan kasar na su koma gidajensu.

Duban mutane da furgaban tashin hankali ya tilastawa tserewa sun bayyana farin cikinsu na gani an lafar da kurar rikicin siyasar Gambia ba tare da Zub da Jinni ba.

Shugaba Adama Barrow da har yanzu ke Senegal ya nada wata tsohuwar ministan Yahya Jammeh, wato Fatoumata Jallow-Tambajang a matsayin mataimakiyar shugaban kasa.

Mai Magana da yawun shugaban kasar Halifa Sallah ya ce an zabi tsohuwar minister ne dan cike gibi ganin yadda nade naden da sabon shugaban kasar ya yi suka karkata gefe guda.

Rahotanni sun ce Fatoumata ta taka rawa wajen hada kan ‘yan adawar kasar dan fitar da dan takara guda da ya kada yahya Jammeh.

Al’amura dai sun soma dai-daita a rikicin siyasar kasar da ya ja hankalin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.