Isa ga babban shafi
Transparency

Rashawa : Najeriya ce ta 136, Nijar ta 101

Kungiyar da ke yaki da rashawa Transparency International ta fitar da rahotonta na shekara game da matsayin rashawa a kasashen duniya. Kungiyar ta yi amfani da alkalumman Bankin duniya da kuma Bankin raya kasashen Afirka a bincikenta kafin fitar da rahoton.

Rahoton Transparency International ya shafi kasashe 176 a duniya
Rahoton Transparency International ya shafi kasashe 176 a duniya transparency
Talla

Bankin Duniya da kuma bankin raya kasashen Afirka ADB na a matsayin madogara da Transparency International ta yi amfani domin jera sunayen kasashen duniya a game da yadda ake karbar rashawa a sassan duniya.

Kasashen New Zealand da Danemark da Finland da kuma Sweden ne a matsayin wadanda suka fi taka rawa wajen rage karfin rashawa a tsakanin al’umma inda suka samu maki da ya kama daga 90 zuwa 80 cikin dari.

Kasashen Jamus da Luxembourg da Birtaniya da kuma Amurka, na cikin kasashen da ke sahu na biyu da makin da ya kama daga 80 zuwa 69 cikin dari a ma’aunin Transparency International.

Sai dai kungiyar mai yaki da rashawa ta bayyana cewa har yanzu wannan matsala na ci gaba da kasancewa a matsayin kadangaren bakin tulu musamman a kasashen masu tasowa.

Libya da Sudan da Sudan ta Kudu da kuma Somalia, na matsayin kasashen da ke can sahun karshe da matsalar ta yin kamari, kuma ga alama babu alamar samun inganci a kasashen lura da rahoton da ya gabata a shekarar bara.

Rahoton ya ce matsalar ta karu a kasashe da dama a shekarar da ta gabata, tare da yin kiran kara daukar matakan yaki da matsalar rashawa a duniya.

Rahoton ya kuma yi kira ga shugabannin kasashen Afrika da suka lashe zabe da niyyar yaki da rashawa kamar Najeriya da su yi kokarin cika alkawalin da suka dauka ga ‘Yan kasa amma ta hanyar bin tsarin dokokin kasa da kaucewa take hakkin dan adam.

Teburin matsayin rashawa a kasashen duniya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.