Isa ga babban shafi
Afrika ta kudu

Jacob Zuma ya fada wani sabon rikicin rashawa

Shugaba Jacob Zuma na kasar Africa ta kudu na shirin fuskantar komitin musamman na jam’iyyar dake mulki ANC gameda da zarge-zarge na cin hanci da rashawa.

Shugaban Africa ta kudu Jacob Zuma
Shugaban Africa ta kudu Jacob Zuma REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Bayyana da zai yi gaban komitin zai kara haifar da rarrabuwan kanu tsakanin ‘yan jam’iyyar ta ANC gabanin babban taron jam’iyyar badi a lokacin da Shugaban Zuma mai shekaru 74 zai sauka daga mulki.

A makon da ya bagata dai ne jam’iyyun adawar kasar Afrika ta Kudu sun bukaci shugaba Jacob Zuma da ya gabatar da sunayen mutanen da ya ce ya sani suna sace kudin kasar.

Wannan ya biyo bayan kalaman shugaban a yankin Kwa Zulu Natal cewar ya san masu sace kudin kasar kuma yana kallon su.

Jam’iyyun adawa na DA da EFF ta Julius Malema sun ce ya zama wajibi ga shugaban ya mika sunayen mutanen ga ‘yan Sanda domin gudanar da aikin su akan wadanda ake zargin.

Shugaba Zuma ya dade yana tsallake rijiya da baya a kokarin tsige shi saboda zargin da ake masa na rub da ciki da kudaden talakawa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.