Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Zuma ya tsallake rijiya da baya

Shugaba Jacob Zuma ya yi nasara a yunkurin ‘yan majalisa na tsige shi daga madafun iko bisa zargin rashawa da kuma yin anfani da kudaden gwamnati don sake fasalta gidan sa ya koma na kasaita.

Ana zargin shugaba Zuma da yin anfani da kudaden gwamnati wajen kawata muhallinsa.
Ana zargin shugaba Zuma da yin anfani da kudaden gwamnati wajen kawata muhallinsa. REUTERS/Mike Hutchings
Talla

 

Shugaba Zuma ya sami goyon bayan ‘yan majalisa dari biyu da goma sha hudu yayin da saura dari daya da ashirin da shida suka nemi a tsige shi

Wannan dai shine karo na uku da ake kokarin tsige shugaba Zuma daga mukaminsa ba tare da samun nasara ba.

Kafin soma kada kuri’ar yankan kaunar a yau Alhamis, jam’iyyar adawa ta Democratic Alliance ta bukaci hadin kan ‘yan majalisar jam’iyyarsa ta ANC domin samun nasarar kawar da shi daga mulki.

Sai dai Jacob Zuma ya sake tsallake yunkurin tsige shi saboda goyon bayan da ya samu daga bangaren Jam’iyyarsa ta ANC da gagarumar rinjaye.

Shugaba zuma dai ya fuskanci zarge zarge na rashawa da kuma anfani da kudadden gwamnati don sake fasalta gidansa ya koma na kasaita.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.