Kungiyar kasashen Africa na taron ta na watanni 6
Shugabannin Kungiyar Tarayyar Africa na shirin zaben sabon shugaban hukumar kungiyar a taron ta na watanni 6 da aka soma yi a yau Litinin a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kasashen kungiyar 54 za su zabi sabon shugaba kasancewar shugaban Hukumar mai barin gado Uwargida Nkosazana Dlamini-Zuma ba ta neman wa'adi na biyu na shugabancin wannan Hukuma.
Yanzu haka dai akwai ‘yan takara 5 dake neman hawa kujeran na tsawon shekaru 4.
Ta kasance mace ta farko data shugabancin Hukumar Kungiyar Africa kuma ana ganin watakila za ta koma gida ne domin neman takaran hawa kujeran tsohon mijinta na shugabancin kasar Africa at Kudu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu