Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Mugabe na bikin cika shekaru 93 da haihuwa

Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe yau na bikin cika shekaru 93 a duniya, yayin da ya sake alkawarin ci gaba da mulkin kasar duk da tsufa da rashin lafiyar da yake fama da su.

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe na bikin cika shekaru 93 da haihuwa
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe na bikin cika shekaru 93 da haihuwa REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Rahotanni sun ce shugaban zai yi bikkin ne shi da ma’aikatan sa a Harare, yayin da magoya bayan sa ke amfani da kafofin yada labaran gwamnati wajen ta ya shi murna.

Sai ranar Asabar za’ayi gagarumin biki a dandalin Bulawayo, inda ake saran dubban mutane su halarta.

A hirar da Jaridar Sunday Mail ta yi da shi, Mugabe ya ce jam’iyyar ta bukaci ya ci gaba da takara, kuma shi bai ga dalilin da ya sa zai ce a’a ba.

Mugabe ya shafe sama da shekaru 30 yana mulkin Zimbabwe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.