Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Ba zan janye daga fagen siyasa ba - Mugabe

Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe wanda ya cika shekaru 93, ya ce ba shi da niyyar janyewa daga fagen siyasar kasar, hadi da ikirarin cewa babu wanda zai iya maye gurbinsa idan har ya janye.

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Mugabe ya ce idan har akwai bukatar ya janye daga fagen siyasa, to kamata yayi kiran ya fito ne daga ‘yayan jam’iyyarsa amma ba ‘yan adawa ba.

Tun a baya ‘yan adawar kasar ke bayyana gazawar Mugabe musamman bisa dalilan rashin lafiya da kuma nisan shekaru, batun da Mugabe ke cigaba da musawa.

Tun a shekara ta 1980 Robert Mugabe ke shugabancin kasar Zimbabwe, bayan samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.