Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Jam'iyyar Zanu-PF ta amince da tazarcen Mugabe

Jam’iyyar Zanu-PF mai mulki a Zimbabwe ta sahalewa shugaban kasar mai ci Robert Mugabe, zama dan takarar ta a zaben shugabancin kasar da za'a yi a shekara ta 2018, dai dai lokacin da shugaban zai cika shekaru 94.

Sugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe
Sugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Tun a shekara ta 1980 Robert Mugabe ke jan ragamar mulkin Zimbabwe, bayan samun ‘yan cin kan kasar daga Birtaniya.

A wannan shekarar dai Mugabe ya fuskanci matsin lambar neman ya sauka daga mukaminsa, sakamakon halin da tattalin arzikin kasar ya tsinci kansa, sai kuma zargin aikata cin hanci da karbar rashawa da ake yiwa jiga jigan gwamnatinsa da masu 'yan adawa ke yi.

Hakan ta sa a watan Yulin da ya gabata, wasu daga cikin ‘yan gani kashenin gwamnatin Mugaben, da suka yi gwagwarmayar neman ‘yanci tare suka juya masa baya.

Wasu daga cikin magoya bayansa dai na neman soke wa'adin shugabancin kasar, domin bawa Mugabe damar mulkin kasa har iyaka rayuwarsa, batun da 'yan adawar kasar suka yi watsi da shi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.