Libya
Tripoli ta dakatar da yarjejeniyar da ta cim-ma da Italiya kan batun yan cin rani
Gwamnatin hadin kai a Libya ta ce, kotun Tripoli ta dakatar da yarjejeniyar da aka cim-ma tsakanin kasar da Italiya kan rage bakin haure da ke shiga Turai.
Wallafawa ranar:
Talla
Friministan Italiya Paolo Gentiloni da takwaransa na Libya Fayez al-Sarraj sun sanya hannu kan wannan yarjejeniya a watan fabrairu don shawo kan safaran bakin haure da ake yi ta kasar da ke arewacin Afrika.
Sai dai kotun daukaka karar Tripoli ta soke amfani da yarjejeniya, tare da bayana cewa majalisar ba ta amince da gwamnatin Fayez al-Sarraj ba
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu