Isa ga babban shafi
Burundi

Burundi: Za'a hukunta masoyan da ke haramtaccen zama

Gwamnatin kasar Burundi ta bai wa dukkanin wasu masoya a kasar da ke zaune da juna ba tare da sun yi aure ba, wa’adin zuwa karshen shekarar da muke ciki, da su tabbatar da an daura musu auren ko kuma su fuskanci fushi na shara’a.

Gwamnatin Burundi zata dukufa wajen tsaftace zamantakewar al'ummarta
Gwamnatin Burundi zata dukufa wajen tsaftace zamantakewar al'ummarta AFP
Talla

Umarnin ya biyo bayan kaddamar da yaki da rashin da’a da gwamnatin kasar, karkashin Pierre Nkrunziza ta yi, domin tsaftace, zamantakewar al’ummar kasar ta Burundi.

Wani mai magana da yawun gwamnatin Nkrunziza, ya ce abin damuwa ne matuka, ganin yadda aka samun yawaitar mata ‘yan makaranta da ke samun juna biyu, ba tare da aure ba, da kuma yadda maza ke neman mata iyaka yawan yadda suka so, a lokaci guda a kasar.

Sai dai kawo yanzu gwamnatin Burundin bata fayyace irin matakin ladabtarwar da zata dauka kan masu haramtaccen zaman ba, amma wata majiya ta bayyana cewa daga cikin matakan ladabtarwar, mai yiwuwa a rika yankawa duk wadanda suka haihu ba ta hanyar aure tara mai tsanani kan kowane jariri da suka haifa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.