Nijar ta ceto ‘yan ci-rani kusan 100 da suka makale a hamada
An ceto mutane 92 a cikin yankin hamada da suka kunshi mata da yara kanana a arewacin Jamhuriyar Nijar, bayan da wadanda ke jigilarsu suka yi watsi da su a kusa da Dirkou.
Wallafawa ranar:
Shugaban ofishin Hukumar Kula da Bakin Haure na MDD a birnin Yamai Giusepe Loperte, ya ce an yi watsi da wadannan mutane ne bayan da suka gaza biyan karin kudade ga wadanda za su tsallakar da su zuwa Libya.
Rahotanni sun ce an ceto mutanen kusan 100 a kusa da Achegour hanyar zuwa Libya.
A farkon watan Juni an tsinci gawarwakin wasu ‘yan ci-rani 44 da suka hada da yara da jarirai a yankin Agadez kan hanyarsu ta tsallakawa zuwa Turai.
A watan Mayu jami’an tsaron Nijar sun taba ceto wasu ‘yan ci-ranin na Afrika a hamada bayan masu fataucinsu sun yi watsi da su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu