An umarci gwamnatin Lagos ta biya mutane diyya
Wata kotu a Najeriya ta umurcin gwamnatin jihar Lagos da ta dakatar da aikin rusa gidajen jama’ar da ke rayuwa a gabar ruwan teku, aikin da gwamnatin ta ce tana yin sa ne domin rage yawan masu aikata laifufuka.
Wallafawa ranar:
A cikin watan Oktoban da ya gabata ne mazauna unguwannin da lamarin ya shafa suka shigar da kara a gaban kotun, bayan da mahukunta suka fara rusa gidajensu, inda hukuncin kotun ya bukaci gwamnati ta shiga tattaunawa da jama’a kan yadda za a biya su kudaden diyya ko kuma inda za su a gaba.
Khadija Yusuf wata da ke rayuwa a irin wadannan unguwanni, ta ce sun yi farin ciki da hukuncin na kotun.
Khadija ta ce rusa matsuguninsu da suke rayuwa a Lagosn ya tursasawa mutane da dama barin garin duk da sun shafe shekaru suna rayuwa domin samun na abinci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu