Isa ga babban shafi
Kenya

An kashe daya daga cikin jami'an da ke shirya zaben Kenya

An kashe wani babban jami’in hukumar zaben kasar Kenya mai suna Chris Msando, wanda ke kula da sashen kula da na’ura mai kwakwalwa a hukumar zaben.

Ranar 8 ga watan Agusta za a gudanar da zaben shugaban kasa a Kenya
Ranar 8 ga watan Agusta za a gudanar da zaben shugaban kasa a Kenya REUTERS/Baz Ratner
Talla

Shugaban hukumar zaben Wafula Chebukati, ya ce alamun da aka tarar a jikin marigayin na tabbatar da cewa an azabatar da shi ne kafin yi masa kisan gilla kwanaki kadan kafin gudanar da zaben shugabancin kasar.

Kisan na zuwa ne bayan hankula sun karkata kan na’urar da za’ayi amfani da ita a zaben na 8 ga watan Agusta sakamakon matsalar da aka samu a shekara ta 2013 wanda ya sanya ‘yan adawa zargin aikata magudi.

Wasu mijoyoyin sun shaidawa kamfanin dilanci labaran Faransa na AFP cewa, Msando ya ba da gagarumin taimakon datse duk wata hanyar samun magudi a zaben na Mako mai zuwa.

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun bukaci a kaddamar da bincike kan kisan Jami’in Zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.