Isa ga babban shafi
Angola

Jam'iyyar shugaba Santos na shirin lashe zaben Angola

Al’ummar Angola sama da mutum milyan tara ne ke kada kuri’a a zaben kasar da ke gudana yau tsakanin ‘yan takarar shugabancin kasar biyu, lamarin da zai kawo karshen mulkin shekaru 38 na shugaba Jose Eduardo Dos Santos. Sai dai alamu na nuni da cewa Jam’iyya shugaba Santos na iya yin nasara a zaben na yau.

Tun da sanyin safiyar yau al'ummar Angola suka fara hawa layin kada kuri'a don kawo karshen mulkin shugaba Santos a kasar dake fama da matsanancin talauci bayan kasancewarta ta biyu a arzikin man fetur kaf Nahiyar Afrika
Tun da sanyin safiyar yau al'ummar Angola suka fara hawa layin kada kuri'a don kawo karshen mulkin shugaba Santos a kasar dake fama da matsanancin talauci bayan kasancewarta ta biyu a arzikin man fetur kaf Nahiyar Afrika Reuters
Talla

Da misalin karfe 6 ne ake saran kulle rumfunan zaben wanda ake fafatawa tsakanin ministan tsaron kasar kuma na hannun daman shugaba Santos Joao Manuel Lourenco mai shekaru 63 daga jam’iyya mai mulki ta MPLA da kuma jagoran adawa na jam’iyyar UNITA da ke bore ga gwamnatin Santos, Isaias Samakuva mai shekaru 71.

A cewar wani matashi Telma Francisco daya kada kuri’arsa a Luanda babban birnin kasar ya shaidawa Reuters cewa tunda sanyin safiya suka kafa layi don ganin sun yi nasarar kawo sauyi a kasar.

A cewar Farancisco mai shekaru 33 ba kowacce jam’iyya ce zata iya jagorancin kasar ta Angola ba.

Rahotannin baya-bayan nan dai na nuni da cewa akwai alamun Laurenco ya yi nasara kan Samakuva lamarin da idan ya tabbata zai mayar da shi shugaba na biyu ga kasar ta Angola mai arzikin man fetur ta biyu a nahiyar Afrika kuma wadda ke fama da matsanancin talauci da karyewar tattalin arziki.

Yanzu haka dai al’umma na tururuwar zaben Joao Lourenco wanda ya yi musu alkawarin yakar cin hanci da rashawa da kuma kawo karshen matsalar tattalin arzikin da kasar ke fuskanta baya ga samar da ayyukan yi ga matasa, haka kuma ya ce yayi da za a fara cin moriyar arzikin man da kasar ke da shi.

Al’ummar kasar dai sun yi amanna da jam’iyyar ta MPLA musamman kan nasarar da ta yi wajen kawo karshen yakin basasar kasar da aka kwashe shekaru 27 ana yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.